Kotun tace Kabiru yana da masaniya gameda shirin kungyar Boko Haram na kai hari kan maja’mi’ar St Teresa. An kashe mutane 44 a harin wasu hamsin kuma suka jikkata.
Kamar yadda kotun ta fada masu gabatar da kara sun tabatar da cewa Kabiru ya kasa ko yaki ya gayawa hukumomi cewa za a kai harin bam din.
Banda ma wannan kotun ta same shi da shirya wasu hare hare ciki harda wani da aka kai a arewacin sokoto.
Ana zargin Kabiru da zama daya daga cikin manyan jami’an kungiyar Boko Haram.Kungiyar da ake zargi da kadamar da yaki domin kafa tsarin shari’a a arewacin Najeria. Kungiyar ce ake zargi da haddasa mutuwar wasu dubban mutane tun lokacinda ta fara tada kayar baya a shekara ta 2009.