Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Ta Amince Da Biyan N71,000 A Matsayin Albashi Mafi Kankanta


Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamna Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnatin jihar ta Kano ta ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwambar 2024.

Gwamnatin Jihar Kano ta amince za ta biya N71,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin karbar rahoton kwamitin tattaunawar ayyukan gwamnati karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan jihar a ofishinsa a ranar Talata.

Ya kara da cewa sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwamba 2024.

Sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ambaci Gwamna Yusuf yana cewa, jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke da dumbin ma’aikatan gwamnati.

"Ina so in jaddada cewa Jihar Kano na da daya daga cikin jihohin masu mafi yawan ma’aikata a Najeriya, duba da irin yawan al’umarmu da bukatunmu na cikin gida da kuma matsi ta fannin kudaden shiga na gida da muka gada, mun yanke shawarar aiwatar sabon albashi na kasa akan N71,000.” Yusuf ya ce.

Gwamna Yusuf ya ce aiwatar da mafi karancin albashi zai kara wa jihar nauyin biyan albashi na wata-wata da sama da Naira biliyan 6, yana mai cewa za a nemi karin Naira biliyan 7 don bukatun kananan hukumomi 44 na jihar.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG