Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Kasar Ivorycost Ta Wanke Simone Gbagbo


Jiya Talata wata Kotu a Ivory Cost ta wanke Simone Gbagbo, matar toshon Shugaban Ivory Coast, wadda aka zarga da laifin cin zarafin bil adama a tashin hankalin bayan zaben 2011.

Ita dai Simone Gbagbo, ba ta a kotun lokacin da aka yanke hukuncin. Masu gabatar da kara na da kwanaki 60 na daukaka kara. Su na bukatar a yanke mata hukuncin daurin rai da rai.

An zargi Simone da jagorantar wata kungiya ta kai hare-hare kan masu adawa da mijinta, tsohon Shugaban kasa Laurent Gbagbo, ciki har da samar da makamai da jirage masu saukar ungulu ma kungiyar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG