Kotun Gauteng, dake kasar Afirka ta kudu ta yankewa wani dan Najeria mai suna Eke Ugochukwu, daurin shekaru ashirin da biyar 25, a sakamakon kama shi da laifin fataucin wata yarinya mai shekaru 25, da haihuwa da kuma tilasta mata yin karuwanci a kasar.
Kotun kuma ta tuhume shi da laifin haddasa aikata yin fyade da ya keta wani sashe naokar gwamnatin kasar na tursasa karuwanci da safarar mutane a daukacin kasar ta Afirka ta kudu.
A cewar alkalin kotun Judge Majake Mabasle, Ugochukwu, zai kwashe shekaru 25 a gidan yari a sakamakon wannan laifin da ya aikata wanda ya taka dokar kasar.
Mujallar Daily Trust ta wallafa cewa akalin ya bayyana cewa "dan Najeriyar ai yi zaman idan yari na shekaru Goma sha Biyar a sakamakon laifin fataucin matashiyar da yayi zuwa kasar , sa annan kuma zai kara asu shekaru Goma na saka ta cikin karuwanci da yayi"
Lauyan Ugochukwu ya bukaci kotun ta tausaya masa bisa la'akari da cewa wannan shine karo na farko da aka taba kama shi da aikata wani laifi a kasar, kuma yana da tsohuwar sa da kuma da wadanda yake dawainiya da su, wanda hakanne ya hana shi shiga harkar saye da miyagun kwayoyi.
Daga karshe alkalin ya bayyana cewa dukkan laifukan da kotun ta kama matashin dan Najeriya da su ba irin laifukan da za a daga wa kafa bane dan haka sai ya yi zaman gidan yari domin hakan ya zama ishara ga wasu.