Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KORIYA TA KUDU: Buhari Ya Mika Sakon Ta’aziyya Ga Gwamnati Da Al'umma


Wasu da suka jikkata
Wasu da suka jikkata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Yoon Suk-yeo, da jama’ar kasar Koriya ta Kudu, da kuma iyalan wadanda suka mutu a wani mummunan turmutsutsun da ya faru a Itaewon da ke gundumar Seoul.

Shugaban ya mika sakon addu’a ga wadanda suka samu raunuka, da kuma ta’aziyya ga daukacin al’ummar kasar, yayin da suke alhinin mutuwar mutane sama da 150 wadanda galibinsu matasa ne da kuma mutanen da basu wuce shekaru ashirin da haihuwa.ba.

Hukumomin agaji sun ce hadarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a yayin da dubban mutane ke halartar bikin al'adar Halloween wanda ake yi a kowace shekara domin bankwana da lokacin bazara da kuma marhabin da shigar lokacin sanyi na hunturu.

Wasu rahotannin sun bayyana yadda wasu 'yan bikin suka rika danne wasu mutanen saboda mummunan matsi har ta kai ga wasunsu na kwance kan wadanda aka danne.

Jami'an lafiya sun ce sauran wadanda suka jikkata ma na cikin mawuyacin hali, inda ake ganin ta yiwu alkaluman wadanda za a rasa su iya karuwa.

Bikin na wannan shekara shi ne na farko tun bayan da aka dage dokar sanya takunkumin yaki da cutar korona.

Gwamnatin kasar ta ce an shiga zaman makoki na kasa baki daya.

XS
SM
MD
LG