Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Na Dab Da Rasa Komai - Shugaba Trump


Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Lahadi ya gargadi shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, akan ayyuka soja masu zafi, duk kuwa da cewa Pyongyang ta ba da sanarwar yin wani muhimmin gwaji a wata tashar harba makamai.

“Kim Jong Un yana da wayon gaske, kuma yana dab da ya rasa komai, idan har ya yi wani abu mai zafi” a cewar shugaba Trump a shafin sa na twitter.

Shugaban na Amurka ya ci gaba da cewa “ya sanya hannu a yarjejeniyar warware shirin nukiliya a Singapore. Ba zai bukaci lalata dangantaka ta musamman tsakanin sa da shugaban Amurka ba, ko kuma yin kutse a zaben shugaban kasar Amurka na watan Nuwamba ba.

Koriya ta Arewa a karkashin shugabancin Kim Jong Un, ta na da tattalin arziki mai karfi da inganci, to amma wajibi ne ta dakatar da shirinta na nukiliya kamar yadda ta yi alkawari. NATO, China, Rasha, Japan da ma daukacin duniya, duk sun yi ittifaki a kan wannan”. In ji shugaba Trump.

Kalaman na shugaba Trump na zuwa ne bayan da kafar yada labaran Koriya suka ce an gudanar da gwaji a tashar harba makamin nukiliya ta 7 a Sohae, tashar harba roka mai cin nisan zango a Tongch’ang ri a yammacin Pyongyang da ke iyaka da kasar China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG