A cewar jami’in, hakan zai iya faruwa ne saboda sauyin shugabancin da za a samu a Amurka da kuma Korea ta Kudu.
Thae Yong-ho, ya kasance jami’i mafi girma daga Korea ta Arewa da ya sauya sheka a watan Agusta cikin shekaru 20 da suka gabata.
A wani taron manema labarai, jami’in ya fayyace cewa ba shi da masaniya kan matakin da shirin gina nukiliyan na Korea ta Arewa ke ciki, amma ya ba da tabbacin cewa, China ba za ta ladabtar da Korea ta Arewan ba game da shirin nukiliyan.
A cikin wannan shekara kadai, Korea ta Arewan, ta yi gwajin makamin na nukiliya har sau biyu, sannan ta harba makamai masu linzami kirar Ballistics sau ashirin.
Baya ga haka ta fito karara ta sha alwashin kaiwa Amurka hari da makamin na nukiliya.