Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Leken Asiri Na Amurka Suna Bayyana Damuwa Kan Rasha


shugaban Amurka Donakd Trump.
shugaban Amurka Donakd Trump.

Darektan hukumar leken Asiri Ta Sojoji ne ya bayyana haka da yake magana da manema labarai

Manyan jami'an hukumomin leken asirin Amurka sun ki su sassauta damuwa da suke nunawa dangane da kasar Rasha, yayinda shugaban Amurka Donald Trump da jami'an Rasha suke bayyana damuwa kan tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

"Manufofi da al'adun mu sun yi karo da juna, " inji darektan hukumar leken asiri karkashin ma'aikatar tsaro Leftanar Janar Vincent Stewart, yayinda yake magana da wasu manema labarai.

Stewart, wand a yayi magana gabannin barkewar sabuwar cacar baki tsakanin shugaba Trump da wakilan majalisun Amurka kan batun na Rasha, ya kuma yi gargadin cewa Moscow tana da zarafin yin katsalandan kuma ta shirya farfagandar da zata biya mata bukata.

A cikin makon nan ne shugaba Trump ya sanya hanu kan sabbin takunkumi da majalisun dokokin kasar biyu suka amince da gagarumar rinjaye. Nan da nan ya hau Twitter yayi zargin cewa danganatak tsakanin kasashen biyu ya tabarbare ainun, amma ya za laifin hakan kan majalisun dokokin kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG