An daga tutar Koriya ta Arewa fiye saman ginin da tawagar ‘yan wasa ke zaune wadanda za su kara a gasar wasannin Olympics a Koriya ta Kudu.
Tutar ta fara kadawa a yau Alhamis a wuraren da za a gudanar da wasannin a biranen PyeongChang da Gangneung wadanda suke da tsawon tafiyar kilomita 230 daga gabashin birnin Seoul, bayan kwana daya bayan bukukuwan bude wasannin da aka yi a kauyukan.
Jinkirin na kwana daya da aka samu ya biyo bayan tsaurara matakan tsaro da Koriya ta Kudu ke da su, wadanda suka hana a daga wata tuta a kasar.
Jami'ai sun cire duk wasu filaye da za’a gudanar da wasannin daga cikin dokar, ciki harda wuraren kwanan ‘yan wasan.
An daga tutar Koriya ta Arewan domin gaishe da 'yan wasanta su 10 wadanda aka sa ran za su isa Koriya ta Kudu a yammacin yau Alhamis.
Za su hadu da mata 12 'yan wasan Kokara na Hockey wadanda suka isa a makon da ya gabata domin su hadu da 'yan uwansan Koriya ta Kudu wajen yin atisaye domin karawa a karkashin tawaga guda.
Facebook Forum