Sweden zata bada taimakon ne ta gayyatar ministan harkokin wajen Korea ta Arewa Ri Yong Hu, ziyarar da masu lura da al’amura a duniya suke ganin zai taimaka wurin shirya ganawa tsakanin shugaban Amurka da na Korea ta Arewa.
Yace tankiyar da ake fama da ita a yankin ruwan Korea, itace babban kalubale da yanzu duniya ta maida hankali akai don haka idan Sweden nada wata rawar da zata iya takawa, shine abin da suke kokarin yi, inji Skoog yana fadawa manema labara a birnin New York.
Minista Ri da Firayi Minista Sweden Stefan Lofven sun yi wata takaitacciyar ganawa a birnin Stockholm na Sweden a jiya Juma’a, kuma mai magana da yawun Lofven yace ba zai yi wani karin bayani a kan abin da suka tattauna ba.
Skoog ya kara da cewa, ana sa ran tattaunawar ta Stockholm zata samar da yanayi mai inganci da zai kai ga shirya ganawar da ake niyar yi tsakanin Amurka da Korea ta Arewa, sai dai yaki amsa tambayar da aka masa, ko Sweden ce zata amshi bakwancin ganawar tsakanin shugabannin biyu.
Yace muna dai bada taimakonmu ne, a kan yanda za a shawo kan tankiyar da ake fama da ita a yankin ruwan Korea.
Facebook Forum