Wasu Jami'an gwamnatin Shugaba Donald Trump sun ce shugaban zai gabata da bukata a gaban Majalisar Dinkin Duniya, cewa idan har hanyar diplomasiyya ba ta yi tasiri ba akan Korea ta arewan, to babu makawa, hakan zai kara yiwuwar daukan matakin soji.
A wata ganawa da aka yi a Fadar White House, Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley tare da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, H.R. McMaster, sun yi lale marhabin da matakin da aka dauka a wannan watan, na kara kakaba takunkumi akan Korea ta arewa, to amma sun ce duk da haka, har yanzu kasar na ci gaba da nuna halayenta.
McMaster ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai a bi tafarkin diplomasiyya, tare da daukan tsauraran takunkumi, idan har ana so a kaucewa daukan matakin soji.
Tawagar da shugaba Trump zai je da ita babban taron na Majalisar Dinkin Duniya a matsayinsa na shugaban kasa, wani abu ne da ba a saba gani ba, domin ta hada har da Mataimakinsa, Mike Pence da Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson da sauran manyan jami’ai.
Facebook Forum