Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofin Duniya: Messi Ba Zai Buga wa Argentina Wasannin Fitar Da Gwani Ba


Messi
Messi

Ita dai Argentina ita take rike da kofin duniya wanda ta lashe a Qatar a shekarar 2022.

Lionel Messi bai zai buga wa Argentina wasannin fidda gwani na neman gurbin shigar gasar kofin duniya ba saboda raunin da ya ji a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Kocin Argentina Lionel Scaloni ya sanar da tawagar ‘yan wasa mai kunshe da ‘yan kwallo 28 a ranar Litinin.

Argentina za ta kara ne da Chile a ranar 5 ga watan Satumba, sai kuma kwanaki biyar bayan hakan ta kara da Colombia.

Shi dai Messi yana fama ne da rauni a kwaurinsa na dama.

Angel Di Maria
Angel Di Maria

Angel Di Maria mai shekaru 36 wanda ya yi ritaya daga bugawa kasarsa ta Argentina kwallo shi ma ba ya cikin tawagar.

Bayan da Argentina ta lashe kofin COPA America ne Di Maria ya sanar da yin ritaya.

Ita dai Argentina ita take rike da kofin duniya wanda ta lashe a Qatar a shekarar 2022.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG