Najeriya za ta shiga sahun masu takarar damar karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afirka ta shekara ta 2025, shekara 25 bayan da ta yi hadin gwiwar karbar bakuncin gasar da Ghana.
Da farko dai an tsara gudanar da gasar ta shekarar ta 2025 ne a kasar Guinea da ke yankin Afirka ta Yamma, to amma kuma rahotanni na bayyana cewa, yanzu haka hukumar kwallon kafar nahiyar ta Afirka wato CAF, tana duba yiwuwar karbe wannan damar.
Shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF Amaju Pinnick wanda ya tabbatar da wannan kuduri, ya ce idan har aka sauya kasar ta Guinea, to kuwa Najeriya za ta shiga takarar karbar bakuncin gasar.
Pinnick ya ce tuni ya sami goyon bayan Ministan wasanni Sunday Dare akan wannan kudurin, inda kuma za su gabatar da bukatar karbar bakuncin gasar na hadin gwiwa da kasa Jamhuriyar Benin.
Najeriyar ta yi hadin gwiwar karbar bakuncin gasar ta shekarar ta 2000 ne da kasar Ghana, inda aka yi amfani da filayen wasa bi-biyu daga kowace kasa. A Najeriya an zabi filayen birnin Ikko da kuma birnin Kano.
Sau 2 ne kacal Najeriyar take samun damar karbar bakuncin gasar ta cin kofin nahiyar Afirka a tarihi, wato a shekarar 1980 da kuma ta 2000.
A Ingila, kungiyar kwallon kafar Arsenal ta bayyana Martin Odegaard a zaman sabon kaftin din ‘yan wasanta, a yayin da ake kammala shirye-shiryen soma sabuwar kakar wasanni ta shekarar 2022 da 2023.
A yanzu matashin dan wasan mai shekaru 23, ya kasance shugaban ‘yan wasan kungiyarsa ta Arsenal, da kuma kasarsa ta Norway, inda ya zama kaftin tun a watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2021.
Odegaard ya koma Arsenal ne na din-din-din daga Real Madrid ta kasar Spain a kakar wasanni da ta gabata, bayan zaman aro na tsawon watanni 6.
Tauraron dan wasan na tsakiya ya haska sosai a kakar wasanni da ta gabata, har ma ya sami kyakkyawan yabo daga mai horar da ‘yan wasan Arsenal din Mikel Arteta.
A kasar Spain kuma sabon cefanen kungiyar Barcelona, Robert Lewandowski, ya musanta rade-radin da ake bazawa, na cewa ya bar Bayern Munich ta kasar Jamus ne saboda yunkurin da ta yi na sayen dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland, da a yanzu ya koma Manchester City ta Ingila.
Lewandowski ya bayyana hakan ne sa’adda yake caccakar tsohuwar kungiyar ta shi ta Dortmund, bisa zargin yin karya akan dalilan sauya shekarsa a wannan bazarar.
Ya bayyana cewa bai taba daukar Haaland a zaman wata barazana ba ko da ya hade da shi a Bayern din, domin kuwa kowa da ta shi gwanintar.
Mai horar da ‘yan wasan Barcelonar Xavi Harnandez dai yayi marhabin da sabbin ‘yan wasan da kungiyar ta saya a wannan bazarar, na baya-bayan nan shi ne dan wasan baya Jules Kounde da kungiyar ta saya daga Sevilla, a yayin da kuma yanzu haka yake dakon zuwan wasu, a daidai lokacin da ake ci gaba da ta’allaka ‘yan wasan Chelsea 2, Ceaser Azpiliqueta da Marcos Alonso da komawa kungiyar.
Saurari cikakken rahoton Murtala Sanyinna: