Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce wani abu da yake ba shi mamaki shi ne yadda ake kashe-kashe da satar shanu a yankin arewa maso yammacin kasar.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnonin jam’iyyar APC da suka kai masa ziyara garin Daura a jihar Katsina kamar yadda kakakinsa Garba Shehu ya fitar a wata sanarwa.
“Abin da ke faruwa a arewa maso yammacin Najeriya shi ne yake ba ni mamaki, saboda za ka ga mutanen da ke zaune tare, yarensu daya, addininsu daya, amma suna kashe kansu tare da sace-sacen shanu.”
“Hakan ya sa sai da na sauya hafsoshin sojoji tare da duba yadda za mu samar da cikakken tsaro. Idan kuka kalli al’amura tare da abin da ke hannunmu, za ku fahimci cewa an samu nasara.”
A cewar Buhari, farashin mai ya fadi da sama da dala 100 inda ya koma dala 38 a karkashin mulkinsa, sannan gangar danyen mai da ake fitarwa a rana ta koma dubu 500, “amma duk da haka mun cimma burinmu da dama.”
Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga masana tarihi da kwararru, da su yi adalci wajen tattarawa da adana bayanan da suka shafi gwamnatinsa, “musamman don a taimakawa masu zabe wajen yin zabin shugabanni na gari.
“Ba daidai ba ne, a batar da masu zabe da karerayi, da son rai,” in ji Buhari yana mai cewa “ya kamata a rika duba abin da zai amfani kasa baki daya.”