A karkashin matakan tsaro masu gaunin gaske a birnin Lahore na Pakistan, an kammala jana’izar gwamnan jihar Punjab da daya daga cikin dogarawan dake gadinsa ya kashe shi.
A nan cikin gidansa na gwamna ne aka bizine Salman Taseer a wannan jana’izar ta hukuma wacce aka guidanar yayinda ‘yansanda ke ta sintiri akan tituna, suna kuma gadin wasu muhimman wurare.
A jiya Talata ne aka harbe wannan gwamnan kuma tuni wani dogarinsa mai suna Mumtaz Qadri ya amsa cewa lalle shine ya hallaka shi saboda bai jin dadin yadda shi gwamnan ya ke ta nuna adawa ga dokokin hana sabo da ake kokarin a kafa a Pakistan.
Ministan harakokin cikin gida na kasar Rehman Malik yace zasu gudanarda bincike don gano ko shi wannan dogarin shi kadai ya kulla kisan ko yana aiki ne da wasu kungiyoyi.
Yau Laraba, wasu malaman addinin Musulunci su 500 suka fitar da wata fatawa a inda su ke yabawa da kisan sannin su ka yi gargadi cewa duk wanda ya yi adawa da dokar hana sabon za a kashe shi shima.
Taseer mamban jam’iyyar Pakistan People’s Party mai mulki ne, wace ke kokarin cigaba da rike ragamar iko