Dimbin matasan kasar suka hallara domin su yi ma shugaban da iyalansa marhaban.
Lokacin da take gabatar da maigidanta ga matasan Mrs. Michelle Obama ta tabbatar masu cewa bayan rikice-rikicen da Ireland Ta Arewa ta yi fama da shi shekara da shekaru matasa a yanzu suna kan gimshiki mai karfi domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasarsu.
Shugaban da matarsa da 'ya'yansu biyu da suka sauka da asubahi sun samu kyakyawar karba. A cikin jawabinsa ga matasan shugaba Obama ya tabo irin munanan matsayi da Ireland Ta Arewa ta yi ta fama da su. Ya ce har yanzu akwai rauni da basu warke ba. Har yanzu akwai jinsuna dake zaman dar-dar domin basu yarda da juna ba.Har yanzu akwai shingaye da suka raba al'umma. Har yanzu akwai tafiya ta milamilai a gabanmu. Ya ce tun da farko muna sane cewa tafarkin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tafarki ne mai nisan gaske. Don haka, inji Obama wannan lokaci ne da zamu tashi cikin gaggawa mu nemi zaman lafiya mai dorewa.
Wakilinmu Sani Dauda nada rahoto.