Kakakin jam'iyyar adawar ta MNSD NASARA Honorabul Tijjani Abdulkadiri ya ce a wannan karon ma ba za su shiga gwamnatin rikon kwarya ba ko da shugaban ya sake kiransu kamar yadda su ka ki a baya saboda har yanzu gwamnati ba ta iya shugabanci ba.
To amma da ya ke mayar da martani wani kusa a jam'iyyar PNDS TARAYYA mai mulki mai suna Alhaji Asumanou Mahammadu ya yi watsi da zargin na jam'iyyar ta adawa, ya ce an sami cigaba sosai musamman ma ta fuskar kare hakkin 'yan kasa da kuma tattalin arziki.