Kashi 50 cikin 100 na wadanda aka gudanar da binciken a kansu, wanda jaridar Washington Post da gidan talbijin din ABC suka gudanar, ya nuna cewa Clinton za ta fi magance matsalar ta’addanci fiye da kashi 39 da ya ce Trump ne zai fi.
Wannan sabuwar kididdiga ta nuna gagarumin sauyi a ra’ayin jama’a, tun bayan hare-haren da aka kai a Paris da San Berndino na California a bara.
Wadanda dalilin su ne Trump ya ce a hana Muslmi shiga Amurka, ya kuma samu karbuwa saboda wadannan kalamai.
Har ila yau mutane takwas cikin goma sun fi nuna damuwarsu kan wadanda su ke kai daidaikun hare-hare na gashin kansu.
Sannan kashi 53 yace ya damu matuka, yayin da kashi biyu cikin uku ya ce ba shi da kwarin gwiwa cewar gwamnatin za ta iya magance daidaikun masu kai hare-hare.