Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Shugaba Amurka Na Afirka Game Da Ilimin 'Ya'ya Mata


Uwargida Michelle Obama, matar shugaban Amurka.
Uwargida Michelle Obama, matar shugaban Amurka.

Uwargidan shugaban Amurka, Michelle Obama, na ziyara a kasar Morocco, a wani mataki na fadada samar da ilimi ga ‘ya’ya mata a duk fadin duniya.

A lokacin da Michelle ta isa kasar, ta samu tarba daga sarauniya Lalla Salma a lokacin da suka sauka da yammacin jiya Litinin a Marrakech tare da ‘ya’yanta mata, wato Malia da Sasha da kuma mahaifiyarta Marian Robinson.

Dukkaninsu sun dunguma zuwa Morocco ne bayan da suka yada zango a Liberia, inda ta halarci wani sansani horar da ‘ya’ya mata kan harkokin shugabanci.

Iinda har ila yau ta gana da shugaba Ellin Johson Sirleaf, mace ta farko da aka fara zaba a matsayin shugabar kasa a Nahiyar Afrika.

Ita dai urwagida Michelle, tana wani tangadi ne na kwanaki shida domin fadada shirinta na ganin an ilmnatar da ‘ya’ya mata ta hanyar kawar da kalubale irinsu auren dole, da talauci da tarzoma da ke sa ‘yan mata miliyan 62 ba sa zuwa makaranta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG