Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Shirin Yakar Cutar Shawara a Kasar Congo


Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, Joseph Kabila
Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, Joseph Kabila

Kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta kaddamar da wani shirin yaki da cutar shawara ko kuma yellow fever, inda za a yiwa mutane miliyan 11.6 allurar rigakafin cutar nan da wata mai zuwa.

Wannan shiri na zuwa ne bayan da aka samu barkewar cutar a babban birnin kasar. A makon da ya gabata, gwamnatin Congo ta ruwaito cewa an samu mutane 67 da ke fama da cutar, kana ana tunanin wasu 1,000 suna dauke da ita.

Barkewar cutar a kasar Angola da ke makwabtaka da kasar, ya kai ga mutuwar mutane 345. Sai dai Ministan kiwon lafiya, a kasar ta Jamhuriyar Congo Felix Kabange, bai bayyana yadda za a samu wadatacciyar allurar rigakafin cutar da za ta isa ko’ina ba.

Ita dai allurar rigakafin cutar ta Yellow Fever ana fama da karancinta a duk fadin duniya, kuma ta kan dauki shekara guda kafin a samar da ita. A makon da ya gabata, hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa tana shirin yin allurar rigakafin ga mutane akan iyakokin kasashen Angola da Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Sannan ta ce tana aiki kafada da kafada da kamfanonin da ke samar da allurar ta yadda za a sa ta wadatu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG