Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci Hukumar Alhazai ta Najeriya da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Saudiyya da su hanzarta tantance adadin ‘yan Najeriya da turmutsutsun Mecca ya shafa don a sanar da ‘yan’uwansu don kuma a dau matakai na gaba.
Wakilinmu na shiyyar Adamawa da ya aiko da wannan rahoton, Ibrahim Abdul’aziz ya ce rahotanni daga Saudiyya na nuna cewa yawan wadanda su ka mutu ya haura 100,000 sabanin alkaluman farko da ke nuna cewa mutane sama da 700 ne su ka mutu. Hasalima ya ce har yanzu akwai wasu alhazan Najeriya da ba a jin duriyarsu. Ganin tashin hankalin da wasu iyalai su ka shiga, an shiga kiraye-kirayen a kwantar da hankali.
Ibrahim ya ruwaito wani dan Majalisar Dokokin jahar Adamawa da a yanzu ke can Saudiyyar mai suna Abdurrahaman Abubakar na kiran da a yi tawakkali. Ya ce al’amarin daga Allah ne don haka bai kamata a dauka cewa kasar Saudiyyar ba ta shirya ba ne. Ya ce Alhazan Adamawa da su ka bace ba wai sun mutu ba ne. Ya ce ai mutum guda ne kadai ma aka tabbatar yam utu. Don haka, in ji shi, sannu a hankali za a same su da ransu.
Tuni dai wasu kungiyoyi da daidaikun mutane ke ta kira ga kasar Saudiyya da ta shiga hada kai da sauran al’ummar Musulmin duniya wajen daukar matakai lokacin aikin hajji ganin abubuwan da su ka yi ta faruwa. To saidai Ibrahim ya ruwaito wani masani mai suna Sheikh Dr Ibrahim Jallo na kiran da a yi kaffa-kaffa kar a fada tarkon masu adawa da hukumar Saudiyya. Ya ce ba ma kasashen Musulmi ba, ko da ma dukkan kasashen duniya ne za su tsara shirin aikin Hajji, ba za su iya kawar da yiwuwar hadari ba. Y ace lallai hatsari bai faruwa sai da sanadi, to amma kuma ya kamata a sani cewa kawar da shi kwata-kwata abu ne mai wuya – to amma ya jaddada cewa shi ba wai kare hukumomin na Saudiyya ya ke yi ba.