Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Kashe Wani Bakar Fata A Jihar Louisiana dake Amurka


Bakake sun yi zanga zangar nuna fushinsu a Baton Rouge
Bakake sun yi zanga zangar nuna fushinsu a Baton Rouge

Amurka ta sake fadawa cikin wani rikicin kashe bakake da 'yansandan kasar ke yawan yi da zara akwai 'yar wata matsala.

Ahalinda ake ciki kuma sashen kula da 'yancin Biul'Adama a ma'aikatar shari'a ta Amurka yace zai jagoranci bincike kan dalilan da suka kai ga 'Yansanda suka harbe suka kashe wani bakar fatan Amurka a harabar wani kantin zamani ranar Talata, a birnin Baton Rouge a jihar Lousiana.

Bidiyon da ya nuna yadda 'yansandan suka kashe mutumin
Bidiyon da ya nuna yadda 'yansandan suka kashe mutumin

Gwamnan jihar Bel Edwards yace hukumar FBI da hukumomin tsaro dake jihar duk zasu taimakawa ma'aikatar shari’an akan binciken da zata gudanar.

Gwamna Edwards ya fada jiya Laraba cewa "na damu ainun. A takaice bidiyon abunda ya faru yana matukar tada hankali."

Bidiyon ya nuna daya daga cikin 'Yansandan biyu yana harbin bakar fatan dan shekaru 37 da haifuwa Alton Sterling, yayinda ake danne da shi. Bidion ya janyo zanga zanga da kuma kiraye kirayen a sallami baturen 'Yansanda garin Carl Dabadie.

A wani taron manema labarai a wani wuri daban , baturen 'Yansanda Dabadie yace "Lokacinda 'Yansanda suka isa wurin, Sterling yana dauke da makami" daga nan ne arangama ko ya kaure da jami'an tsaro.

XS
SM
MD
LG