A ci gaba da neman hanyoyin da zasu bada damar wanzar da zaman lafiya, kasashen yankin tafkin Chadi sun bukaci dala biliyan 12 domin gudanar da ayyukan inga ci gaban jama’ar da matsalolin boko haram suka jefa cikin tashin hankali.
Ganin cewa amfani da karfin soja kadai ba zai warware matsalolin dake da nasaba da rikicin Boko Haram ba ya sa kasashen CBLT wato Nijer, Najeriya, Chadi, da Kamaru suka fara hangen bullowa lamarin ta wasu hanyoyin na daban wadanda a karkashinsu za a dauki matakan inganta rayuwar jama’ar da wannan ala’amari ya afkawa.
Kungiyar kasashen tafkin Chadi tana bukata miliyoyin Dalar Amurka a cikin shekaru biyar masu zuwa domin gudanar da ayyuukan da ta sa gaba na ci gaban jama’ar lardunan da rikicin na Boko haram ya shafa.
shugabanin al’umma sun yi na’am da wannan yunkuri da suke ganin zai tayarda komadar da hare haren ta’addancin suka yiwa tattalin arzikin jama’ar yankunan da suka tsinci kansu cikin wannan hali.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma
Facebook Forum