Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Koka Da Kisan Fararen Hula a Yankin Tafkin Chadi


Wani sojan kasar Jmahuriyar Nijar, yayin da yake tabbatar tsaro a wani yanki na Diffa. Yuni 18, 2016.
Wani sojan kasar Jmahuriyar Nijar, yayin da yake tabbatar tsaro a wani yanki na Diffa. Yuni 18, 2016.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya, sun nuna matukar damuwa kan yadda ake samun karin tashe-tashen hankula masu nasaba da rikicin Boko Haram a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar.

Jami’an sun ce, mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutum 88 a yankin Tafkin Chadi a watan da ya gabata kadai, inda suka ce a bara, mutum 107 a daukacin shekarar 2018.

Kakakin ofishin da ke kula da fannin ba da tallafi ga wadanda rikici ya rusta da su, Jens Laerke, ya ce, karuwar adadin da aka gani, na da nasaba da yadda kungiyar mayakan ta Boko Haram ta sauya dabarun kai hare-harenta.

“Ba wai mayaka ne da ke dauke da makamai suke yakar wasu mayakan masu dauke da makamai ba, a’a, mayaka ne da ke yakar fararen hula, da suka hada da mata da yara kanan, wannan kuma babban abin damuwa ne.” Inji Laerke.

Ya kuma kara da cewa, daga cikin mutum 88 da suka mutu a watan na Maris, har da mutanen da ke gudun hijira a wasu yankuna.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG