Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Sun YI Kira A Kare Hakin Bil'adama a Afrika


Tmbarin Kungiyar Human Rights Watch
Tmbarin Kungiyar Human Rights Watch

Kungiyar kwato 'yancin bil adama ta gudanar da taro a kan muzgunawa dan adam da ake yi a duniya, musamman a nahiyar Africa inda lamarin ya fi kamari.

Kasashe sama da arba’in suka halarci babban taron karawa junan sanin domin daukar matakan shawo kan cin zarafin bil’adama.

Kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da Kungiyar Tarayyar Turai, da kungiyar Common Wealth. Mahalarta taron sunce lallai ne a hada karfi da karfe wajen shawo kan wannan matsalar. Mahalarta taron sunce mata da kananan yara ne suka lamarin yafi shafa a kasashen nahiyar Afirka wadanda a duk lokacin da aka sami tashin hankali, suke shiga mawuyacin hali, wadanda kuma ake saurin amfani dasu a matsayin sojojin sa kai ko kuma a tilasta masu kai hare haren kunar bakin wake.Wadansu hanyoyin da ake tauyewa mata shine, ta wajen yi masu fyade.

Wata mata da wakilin Sashen Hausa ya yi hira da ita tace yanzu an daina aure dole sabili da ana ba mata damar zaben wanda suke so su aura ta kuma bayyana cewa, zata bar ‘ya’yanta mata su zabi wadanda suke so su aura.

Wakilinmu Mohammed Awal Garba ya ruwaito cewa, duk da yake an sami ci gaba a wadansu fannoni kamar yiwa mata kaciya da kuma batun auren dole, ana keta hakin fursunoni a gidajen yari da daman a nahiyar Afrika

Ga cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG