Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Turkiyya Ta Ce Saudi Ta Kahe Jamal Khashoggi


Hukumomin a Turkiyya sun hakikanta cewa, an kashe wani Dan-jaridar kasar Saudi Arabiya dake gudun hijira a Amurka bisa radin kanshi, a ofishin jakadanci Saudiyya dake Istanbul, a lokacin da yaje don karbar takardun auren shi.

Hukumomin Saudiyya sunce wannan zargin bashi da tushe, duk dai da cewar ba’a ga Dan-jaridar ba, mai shekaru 59, Jamal Khashoggi, na tsawon kwanaki.

Matar da Jamal zai aura Hatice Cengiz, ta ce ta jirashi a bakin ofishin ranar Talata, amma bai fito daga ofishin ba.

Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan, ya shaidawa manema labarai jiya Lahadi cewa, “Ina bin Kadin aika-aikan, kuma zan sanarwa duniya duk abun da muka samu daga ofishin” Insha Allah ba zamu shiga cikin munmunan yanayi da bamu so ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG