Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kataloniya Ta Ayyana 'Yanci Daga Spain; Spain Ta Rusa Gwamnatin Yankin Kataloniya


Tutar Cataloniya na kadawa
Tutar Cataloniya na kadawa

Kallo ya koma sama a kasar Spain, inda gwamnatin Spain da gwamnatin yankin Kataloniya su ka sa kafar wando guda. Yanzu ba a san wanda zai riga dayan cire kafarsa ba. Yayin da Katalan ta ayyana 'yancin kai, ita kuma Spain ta ce hatta dan ikon da ta bai yanki na Kataloniya yanzu ta janye.

Jiya Jumma'a Majalisar Dokokin Yankin Kataloniya (Catalan) ta kada kuri'ar ayyana 'yancin kai daga kasar Spain, ta na mai amincewa da shawarar da aka yanke a hukumance, ta kiran taron assasa kundin tsarin mulki, wanda zai kai ga kafa janhuriya mai diyauci. Nan da nan bayan sanar da sakamakon kuri'ar, sai majalisar ta game da sowa, 'yan Majalisar na ta rungumar juna saboda farin ciki, su na ta raira taken kishin yankin na Catalan.

Bangaren masu tsattsauran ra'ayin aware na gamayyar yankin na Catalan bisa jagorancin Shugaban yankin na Catalan Carles Puigdemont ne ya rubuta daftarin shawarar ballewa daga Spain ya gabatar ga Majalisar, inda ya samu amincewa da kuri'u 70 akasin 10; sai kuma kuri'u biyu na marasa ra'ayi.

Jam'iyya mai mulki ta masu sassaucin ra'ayin rikau, Popular Party; da kuma jam'iyyar adawa ta masu sassaucin ra'ayin gurguzu, socialists party; wadanda ke da kusan rabin kujerun Majalisar Dokokin ta Catalan, sun kaurace ma kada kuri'ar.

Wannan matsayin da Majalisar Dokokin yankin na Catalan ta dauka jiya Jumma'a, ya kawo karshen rashin tabbas game da makomar batun 'yancin kan na Catalan, wanda ya dada amo bayan kuri'ar raba gardamar da aka kada ranar 1 ga watan nan na Oktoba, inda aka samu kashi 90% na amincewa a kuri'ar, wadda kashi 50% na masu rajistar zabe ne kawai su ka kada.

Tuni kasar Spain ta mai da martani da rusa gwamnatin yankin na Cataloniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG