A cewar wani babban alkali mai shigar da kara a babbar kotun birnin Kwanni da sunan gwamnatin kasar, Malam Musa Haruna, yace matasa ne ke shan kwaya kuma kasa bata ginuwa sai da matasanta.
Alkalin yace dalili kena gwamnatin ta tashi tsaye akan lamarin kuma tana kira ga matasa da su bar wannan dabi’a da zata nakasar dasu idan suka cigaba. Ya zama wajibi a dakile shigo da kwaya kasar.
Yace a wannan shekarar sun kama masu kwaya da dama . Sun kuma kama wadanda suke sayarwa har da ma wadanda suke daukowa daga kasashen waje suna shigo da ita kasar. ‘Yansanda da jandarmomi suna kokari kuma suna cigaba da kama duk masu wannan muguwar sana’a.
A nashi bangaren shugaban kungiyar masu sufuri na birnin Kwanni yace jami’an tsaro na kawo masu taimako a tashoshinsu na daukan fasinjoji inda matasan suka saba boyewa a ciki suna aikata muguwar dabi’ar ta sha da sayar da kwaya.
Masu sufuri su ne sukan kira ‘yansanda idan suka lura cewa matasa na shan kwaya kuma barayi sun soma yi masu yawa. ‘Yansandan suna samun nasarar kama matasan.
Yanzu dai matsayin gwamnatin Nijar ita ce duk wanda aka kama da sunan kwaya to gidan kaso ya nufa.
Ga karin bayani.