Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uganda na tuhumar wani dan adawa da laifin cin amanar kasa


Dan adawa, ftaccen mawaki kuma dan majalisa Kyagulanyi Ssentamu, da aka fi sani da Bobi Wine, shi ne ake tuhuma da laifin cin amanar kasa a Uganda
Dan adawa, ftaccen mawaki kuma dan majalisa Kyagulanyi Ssentamu, da aka fi sani da Bobi Wine, shi ne ake tuhuma da laifin cin amanar kasa a Uganda

Robert Kyagulanyi mawaki da aka fi sani da suna Bobo Wine yana fuskantar tuhuma akan laifin cin amanar kasa inji mahukumtan Uganda

Wani dan majalisar dokokin kasar Uganda na bangaren ‘yan adawa, wanda asalinsa fitaccen mawaki ne, na fuskantar tuhuma kan laifin cin amanar kasa, bayan da hukumomi suka yi watsi da wata tuhuma da ake masa kan wasu makamai.

Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine a harkar waka, ya bayyana ne a gaban wata kotun soji a jiya a arewacin garin Gulu, domin fuskantar tuhumar da ake masa kan makaman.

Kotun dai ta yi watsi da cajin, amma kuma nan take ‘yan sanda suka sake tsare shi, inda aka shigar da wata sabuwar tuhuma akansa, ta cin amanar kasa.

Alkalin kotun ya sa a tsare dan majalisar a gidan wakafi, har sai ranar 30 ga watan nan na Agusta.

A makon da ya gabata aka kama Kyagulanyi tare da wasu ‘yan majalisa hudu, inda ake zarginsu da hannu a wani hari da aka kai akan jerin gwanon motocin shugaba Yoweri Museveni a garin Arua.

Akwai zargin cewa masu zanga zanga sun yi wa ayarin motocin na Museveni Shewa tare da jifansa da duwatsu, a lokacin yana kyamfe a zaben maye gurbin wani dan majalisar yanki.

A lokacin, Kyagulanyi, yana yankin a yana yi wa wani dan takara a bangaren ‘yan adawa kyamfe.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG