Kamaru ta yi nasarar samun tikitin zuwa Qatar ne bayan da ta doke Algeria a wasan neman gurbin shiga gasar, inda dan wasanta Karl Toko Ekambi ya zama zakaran Kamaru da ya zura kwallo ana gab da kamala fafatawar yayin da wasan ya shiga karin lokaci.
Babban matsayi da Kamaru ta taba kaiwa a gasar cin kofin duniyar shine kwata final a shekarar 1990, lokacin da ta burge masu sha’awar kwallon kafa a fadin duniya da irin salon taka ledarta mai nishadantarwa.
Babban aiki dake a gaban Kamaru yanzu kara azama kan wasanta shine sakata cikin rukuni da ake gani mai karfi tare da Brazil da ake kyautata mata zato, da Serbia da kuma Switzerland
Taranga Lions tana da kwararrun ‘yan wasa a cikin tawagarta, wadda take gani zata bada mamaki a gasar ta wannan watan Nuwamba.
Jerin sunayen karshe na ‘yan wasa 26 na tawagar Taranga Lions da kungiyoyin da suke wasa sun nuna:
Gololi sun hada ne da: Devis Epassy (Abha Club), Simon Ngapandouetnbu (Olympique de Marseille), Andre Onana (Inter Milan)
‘Yan wasan baya su ne: Jean-Charles Castelletto (Nantes), Enzo Ebosse (Udinese), Collins Fai (Al Tai), Olivier Mbaizo (Philadelphia Union), Nicolas Nkoulou (Aris Salonika), Tolo Nouhou (Seattle Sounders), Christopher Wooh (Stade Rennes)
Wadannan su ne ‘yan wasan tsakiya: Martin Hongla (Verona), Pierre Kunde (Olympiakos), Olivier Ntcham (Swansea City), Gael Ondoua (Hannover 96), Samuel Oum Gouet (Mechelen), Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli)
Masu wasan gaba su ne: Vincent Aboubakar (Al Nassr), Christian Bassogog (Shanghai Shenhua), Eric-Maxime Choupo Moting (Bayern Munich), Souaibou Marou (Coton Sport), Bryan Mbeumo (Brentford), Nicolas Moumi Ngamaleu (Young Boys Berne), Jerome Ngom (Colombe Dja), Georges-Kevin Nkoudou (Besiktas), Jean-Pierre Nsame (Young Boys Berne), Karl Toko Ekambi (Olympique Lyonnais)
Zakaru 11 da zasu takawa Kamaru leda da irin salon wasa na (4-3-3), sun hada da, Onana; Fai, Castelletto, Nkoulou, Tolo; Hongda, Gouet, Ondoua; Mbeumo, Aboubakar, Toko Ekambi.