Wannan batu dai na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke dauka na samar da wani asusu, da za a rinka amfani da shi wajen gyara hanyoyin mota na Najeriya, wadanda ke zama tamkar tarkon mutuwa ga matafiya.
Yanzu haka dai akwai kudurin dokar kafa wannan asusu a gaban Majalisar Dattawan Najeriya, wadda kwamitinta na ayyuka da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ke jagoranta, ke duba yiwuwar ‘kara farashin Man Fetur da kuma dawo da shingayen biyan harajin amfani da hanyoyi a matsayin samar da kudaden shiga ga wancan sabon asusun da za a kafa.
A cewar wani direba mai suna Isa Saleh, maganar karin kudin mai ma bata taso ba, domin idan zai yiwu suna bukatar gwamnati ta rage kudin Man Fetur din daga 145 zuwa 100.
Shi kuma Alhaji Jamilu Kaira, kira yayi ga gwamnati da ta taimaka wajen yin hanyar ba tare da ta ‘karbi ko sisin kwabo ba daga direbobi, ganin yadda ‘kasar ke da arzikin da zata iya yin hakan.
Shi kuwa Ahmed ‘Yankwashi, na ganin samar da shingaye biyan kudaden harajin amfani da hanya abu ne mai kyau idan har sauran jami’an tsaro dake kan hanyoyi zasu daina karbar kudade daga hannun direbobi.
Tuni dai kungoyoyin gwagwarmaya ke cewa sunyi nazarin makomar talakan Najeriya karkashin wannan sabon yunkurin. Shugaban kungiyar bibiyar hakokin ‘yan Arewa ta Arewa Concern Citizens, Barista Audu Bulama, yace a baya an ‘kara farashin Man Fetur ne da zummar idan komai ya daidaita za a saukar da farashin, sai gashi yanzu wasu ‘yan Majalisa na neman a kara farashin.
Sai dai har yanzu kungiyar mamallaka manyan motocin dakon kaya da galibin ‘yan Najeriya ke ganin suna taka rawa wajen lalata hanyoyi a kasar ta yi shiru.
Domin karin bayani ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum