Buratai dai ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar takardun shaidar kirkiro wannan jami’a daga hannun gwamnan jihar Borno Kashim Shettima. Ya ce da yardar Allah a cikin wannan shekara ne za a bude jami’ar, wadda za ta amfani mutanen Borno da duk ‘yan Najeriya baki ‘daya.
A cewar babban hafsan, jami’ar da ake shirin kafawa za ta zama jami’ace ta musamman, domin za ta zama wata cibiya ta warware irin matsalolin da ake fuskanta. Haka kuma jami’ar ba zata zamanto ta soja ba ce kadai, duk ‘yan Najeriya zasu iya shigarta.
Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce batun ilimi abune da kowacce al’umma dake son ci gaba ya kamata ya zamanto na farko garesu. ya kuma ce irin wannan yunkuri da Buratai yayi na kafa jami’a abune da ya kamata ace duk wani mai kishin ‘kasa ya yi.
A cewar gwamnan wannan jami’a kadai zata iya samar da ayyukan yi ga dinbin matasan Najeriya da ke zaman banza. Haka kuma gwamnan ya tabbatar da bayar da goyon baya ga kafa wannan jami’a dari bisa dari.
Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda Biu.
Facebook Forum