Yada rahotannin karya a kafofin sadarwa na zamani suka zama tamkar ruwan dare gama duniya a yanzu, musamman a Najeriya inda mutane kan yada rahotannin da ba'a tantance ba ko kuma na karya ya sa gwamnati tayi alkawarin daukan matakan dakile lamarin.
Kwana kwanan nan an baza rahotanni a Legas cewa ana wani mummunan rikici a unguwar Oshodi amma kuma lamarin ba haka yake ba.
A can baya an taba bada rahoton mutuwar Shugaba Muhammad Buhari kuma shi ma kamar na Oshodi labarin karya ne.
A wata sanarwa da ministan yada labarun Najeriya Lai Muhammad ya fitar a Abuja yace gwamnati ba za ta lamunta da duk wasu masu bada rahotannin karya ba. Yana mai cewa gwamnati zata dauki mataki a kansu. Yace masu baza rahotannin karya suna yin hakan ne domin tada hankulan al'umma.
Akan ko akwai wani matakin da gwamnati za ta iya dauka akan masu baza rahotannin karya Dr. Danlami Alhassan dake koyas da aikin jarida a Jami'ar Bayero dake Kano yace matsalar ita ce kundun tsarin mulkin kasa ya ba kowane dan kasa 'yancin fadin albarkacin bakinsa da yada ra'ayinsa da manufofinsa. Babu abun da za'a yiwa mutum idan dai ba ya batanci wani ba ko ya bata masa suna ba. Yada wani labari ba laifi ba ne.
Mr Tajudeen wani dan kasuwa ne a tashar Oshodi ya karyata batun samun rikici a unguwar. Yace suna cikin zaman lafiya.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum