Sabuwar gwamnatin da Janar Buhari zai kafa watan gobe zata duba batun take hakin bil Adama da ake zargin jami'an tsaro da yi musamman a arewa maso gabas, yankin da yake fama da ta'adancin Boko Haram.
Janar Buhari ya bayar da tabbacin ne a karshen ziyarar da ya kai jihohin Bauchi da Gombe domin gode masu da zabensa da suka yi.
An ce matsalar take hakin mutane da jam'ain tsaro ke yi abu ne da ya zama ruwan dare kuma wai sun dade suna aikatawa a cikin kasar ta Najeriya. Wadanda suke tsare a hannunsu sun fi shan azaba.
Janar Buhari yace gwamnati tana kashe makudan kudi akan horoas da jami'an tsaro da samar masu kayan aiki tare da biyansu albashi domin su kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Janar Buhari yace horon da aka basu da kayan aiki saboda su kare kasa ne da mutanenta ba su kuntuntawa kowa ba.
Masu rajun kare hakin bil Adama sun ce idan gwamnatin Buhari ta yi hakan zai zama daratsi ga kowa musamman jami'an tsaro da masu rike da madafin iko da kuma na gaba. Barrister Abdullahi Muhammad Inuwa, lauya mai zaman kansa kuma mai fafitikan kwato 'yancin bil Adama, yace idan aka ladaftar da wadanda suka keta hakin mutane zai zama gani ga wani zai sa wani tsoron Allah. Idan hakan ya faru to gaba ba zasu sake yi ba.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.