Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Agogon Apple Mai Aiki A Madadin Waya


Sabon Agogon Kamfanin Apple
Sabon Agogon Kamfanin Apple

Mafi akasarin kamfanoni masu kera wayar hannu da agogon hannu, da akan iya hada su don aiki tare, kamar wayoyi Samsung da iPhone kan haddu da agogon Apple, wajen karantawa da aikawa da sakon gaggawa.

Da yawa wayoyin da agogunan suna aiki a lokacin da aka ajiye su a kusa da juna, duk lokacin da aka nesanta su, ba zasu dinga samun ganawa don aiki tare ba. Kamfanin Apple, zasu kaddamar da sabon agogon su, da yake aiki daban.

Sabon agogon Apple zai dinga aiki da wayar iPhone, koda kuwa wayar bata kusa da agogon, abu kawai da mutun yake bukata shine, ya zamana agogon yana da tsari layin waya da za'a bashi.

Wannan kuma wani abu ne da mutun zai danganta shi, da kamfanin da suke bashi sabis, kamar kamfanin da mutun yake amfani da layin su. Agogon za’a bashi lambar shi ta musamman, amma akwai yadda za’a danganta lambar agogon da na wayar mutun.

A duk lokacin da aka kira mutun, kodai ta layin wayar shi ko ta layin agogo wayar zata shigo cikin agogon, da kuma sanin waye ya kira kamin dauka, domin suna zai fito kamar yadda yake fitowa a wayar hannu.

Wannan wani sabon tsari ne da zai ba mutane, damar fita ba tare da daukar waya a hannu ba, domin kuwa duk abun da mutun zai yi da waya, zai iya yin shi da agogon hannu.

A gobe Juma’a idan Allah ya kai rai, kamfanin Apple zasu kaddamar da sababbin agogunan guda uku, wanda kudin su zai fara daga dallar Amurka $400, dai-dai da naira dubu dari da hamsin. Agogon mai karancin kudi kuwa za’a siyar da shi akan dallar Amurka $250.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG