Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Meta Ya Kaddamar Da Manhajar Muhawarar Sada Zumunta Mai Suna Threads A Matsayin Kishiya Ga Twitter


META-THREADS/
META-THREADS/

Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, ya kaddamar da sabuwar manhajar sa ta Threads, manhajar sada zumunta da ke da nufin yin adawa da shaharar manhajar Twitter malllakar daya daga cikin masu kudin duniya Elon Musk.

A cikin sa'o'i da fitowar ta, Threads nan take ta yi nasarar samun masu rajista kimanin miliyan 10, al’amarin da yazo da ban mamaki, hakan na nuni da babban kalubale da yake gaban shahararriyar manhayajar Twitter, musamman la’akari da irin korafe-korafe da ke zagaye da ita cikin dandalin sada zumunta na duniya.

META-THREADS/
META-THREADS/

A cewar Zuckerberg, an fito da manhajar ne domin ba kowa damar fadin ra’ayinsa da abin da ke zuciyar sa ba tare da wata tangarda ba wanda kowa ke burin ganin irinsa a fadin duniya.

Zuckerberg ya cigaba da bayyana cewa, manhajar Threads tayi nasarar tara rajista sama da miliyan 10 a cikin sa'o'i bakwai na farkon fitowar ta, wanda ke nuni da babban matakin sha'awa da yuwuwar samun nasara.

Meta - Threads
Meta - Threads

Nasarar Thread an danganta shi da ikon Meta na yin amfani da babban tushen runbun jama’a da ta tara a dandamalin ta kamar Facebook da Instagram, wanda yake baiwa masu amfani da manhajojin damar bude shafin Thread nan take ba tare da sabon rajista ko shan wahala ba.

Samun miliyoyin jama’a nan take a wannan manhaja da cigaba da karuwar su na nuni da irin tasiri da karbuwar da manhajar zata yi da kuma haifar da hasashe game da yuwuwar tasirin zauren zai iya yi akan Twitter, wanda ya dade yana rike da karfi a sararin kafofin sada zumunta na zamani.

A cewar Zuckerberg, Twitter ta sami dama amma bata yi amfani da ita ba, amma ya tabbatar da cewa su zasu yi amfani da tasu damar ta hanyar da ta dace.

Mark Zuckerberg da Elon Musk.
Mark Zuckerberg da Elon Musk.

Sai dai akwai fargaban cigaba da tattara bayanai muhimmai kamar yadda abokan gogayya da kamfanin Meta suka yi, musamman bangaren bayanai da suka shafi kasuwanci, kudi da lafiya.

Yayin da labarin nasarar Threads ya bazu, Elton Musk, shugaban kamfanin Tesla da SpaceX kuma mai mallakin kamfanin Twitter ya yi amfani da Twitter ya bayyana shakkunsa. Musk ya soki kamannin manhajar Thread din da Twitter.

META-THREADS/
META-THREADS/

Har ila yau, kamfanin na Twitter ya sake nanata kudurinsa na samar da yanayi mai aminci da jan hankali ga masu amfani da shi, tare da jaddada ci gaba da kokarin da yake yi na inganta manhajar da masu amfani da ita.

A yanzu haka ana iya sauke wannan manhaja ta Thread wanda aka yita don muhawara na fagen dandalin sada zumunta na zamani a sama da kasashe 100, kamar su kasar Amurka, Birtaniya da sauran su, amma ban da kasashen Tarayyar Turai.

Yayin da manhajar Thread ke ci gaba da samun karbuwa, hakan zai sanya ta cigaba da haifar da gagarumin kalubale ga Twitter a sararin dandalin sada zumunta na zamani.

Watannin masu zuwa su zasu tabbatar da ko manhajar ta Thread zata iya karbe ragamar daga hanun Twitter ko akasin haka.

~ Yusufuddeen Aminu

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG