Kwamitin Harkokin Tsaro Na Majalisar Wakilan Najeriya sun kai ziyara a jahar Borno, don gane ma kansu ta’asar da ‘yan ta’adda su ka tafka don kuma su jajanta ma wadanda abin ya rutsa da su da kuma jin ta bakin sojojin da ke yaki da ‘yan ta’addan.
Da ya ke tarbar tawagar Majalisar Wakilan Tarayyar ta Najeriya, Gwamnan jahar ta Borno, Furfesa Babagana Umara Zulum ya ce ya lura cewa babbar matsalar sojojin Najeriya ita ce rashin kayan aiki. Ya ce ya kamata wadanda abin ya shafa su saurari bukatun sojojin Najeriya su biya masu bukata saboda su samu sukunin fatattakar ‘yan ta’addan kowa ya huta.
Gwamnan y ace ya kamata a kara sojojin Najeriya da wajen dubu dari, kuma a dau ‘yan asalin yankin na Borno a matsayin sojoji don kare yankin. Ya ce bai ma kamata a yi la’akari da nisan karatun Bokon mutum kafin a dauke shi aikin soji ba. Ya ce har ma wadanda bas u yi Boko ba, matukar ‘yan yankin ne, to a dauke so aikin soja saboda su kare yankin.
Tawagar Majalisar Wakilan ta ce bisa ga abubuwan da ta gani da kuma ji a ziyarar da ta kawo a jahar ta Borno, za ta dau mataki a majalisance na ganin sojojin sun samu biyan bukata saboda su yi aikinsu yadda ya kamata.
Ga wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, da cikakken rahoton:
Facebook Forum