‘Yan wasan Indomitable Lions na kasar Kamaru sun kai zagayen semi-finals a gasar cinn kofin nahiyar Afirka da ake yi a kasarsu.
Kamaru ta cimma wannan matsayi ne bayan da ta doke Gambia da ci 2-0.
Dan wasan Kamaru Toko Ekambi ne ya zura kwallayensa biyu a ragar Gambia cikin mintina bakwai bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a filin wasan Japoma da ke birnin Douala.
Ita ma Burkina Faso ta bi sahun Kamaru, bayan doke Tunisia da ci 1-0, ta hannun dan wasanta Dango Ouattara gab da za a tafi hutun rabin lokaci.
Ko da yake, alkali ya ba Ouattara jan katin sallama a minti na 82 saboda mahangulba da ya yi wa mai tsaron bayan Tunisia Ali Maaloul.
Hakan ya sa Burkina Faso ta karasa wasan da ‘yan kwallo goma cikin mintina goma da suka rage a wasan.
Kamfanin dillancin labaran AP ya rauwaito cewa ‘yan wasan na Burkina Faso sun barke da murna a lokacin da alkalin wasan ya hura tashi a filin wasan na Garoua.
A farkon wannan mako sojoji suka yi juyin mulki a kasar ta Burkina Faso, wani lamarin da wasu suka yi fargabar zai iya shafar nutsuwar ‘yan wasan, amma sai ga shi sun kai ga gaci.
A ranar Lahadin nan, Egypt za ta kara da Morocco Senagal kuma ta fafata da Equatrial Guinea a saraun wasannin quarter-finals.