Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Amurka Zai Su Iya Shafar Tattalin Arzikin Najeriya – Mohammed Idris

Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)
Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)

A makon da ya gabata Amurka ta fitar da gargadi ga ‘yan kasarta da ke zaune a Najeriya inda ta yi kira a gare su da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar "fuskantar barazana” a wasu manyan otel-otel din biranen kasar.

Gwamnatin Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan gargadin da Amurka ta yi wa ‘yan kasarta mazauna Najeriya kan su yi taka-tsantsan yayin da suke zaune a kasar.

Hukumomin kasar sun ce gargadi irin wannan zai haifar da rudani ya kuma shafi tattalin arzikin kasar a cewra jaridar Daily Trust.

A makon da ya gabata Amurka ta fitar da gargadi ga ‘yan kasarta da ke zaune a Najeriya inda ta yi kira a gare su da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar "fuskantar barazana” a wasu manyan otel-otel din biranen kasar.

Ko da yake, shawarar da Amurkar ta bayar har ila hau ta ce jami’an tsaron kasar na daukan matakan dakile duk wani hari.

Yayin da yake wani jawabi a Abuja, babban birnin Najeriya, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce wannan gargadi da Amurkar ta fitar zai iyara mayara da hannu agogo baya a yunkurin da gwamnati ke yi na janyo hankulan masu saka hannayen jari.

Ya kara da cewa, gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta kare lafiyar dukkan masu ziyarar a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG