Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zasu Kawar da Bara a Tsakanin Almajiran Allo


Almajiri
Almajiri

Matsalar barace barace ga yara masu karatun Allo a yankin arewacin Najeriya, matsala ce da ta dade ana fafutukar magance ta duk da cewa dai akwai dan banbancin ra’ayi a tsakanin Malamai, game da barar Almajiran Allon.

A baya dai hukumomi sun yi ta yin yunkurin kawar da ita amma lamarin ya gamu da cikas, a yanzu haka dai wata sabuwar kungiyar mahaddata Al-Qur’ani, da suka yi karatu a makarantun tsangaya sun lashe takobin ganin cewa sun kawar da bara a tsakanin Almajiran Allo.

Sheikh Hassan Musa, shine shugaban kungiyar a Najeriya, kuma yace “Mu maganar barar da muke Magana itace bara ta kananan yara wadda idan aka duba, Almajirai, ‘yan tsangaya, da suke bara a Kantuna, da Tituna da Tashoshin mota da wurin da duk bai dace ba za’a ga shekarun su baya wuce goma sha biyar ba, to wannan barar itace muke Magana akai itace kuma ta kawo mu.”

Jama’a da dama dai na cike da fatan ganin sabuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari, zata yi na mijin kokarin da zai kai ga rage yawon barace barace a tsakanin yara masu karatun Allon, ta hanyar wadata kasa da abinci da kuma wani tsari na masamman.

XS
SM
MD
LG