Harkokin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen na fuskantar karancin kudi, kuma dole kwanan nan a rage adadin kayan abincin da ake bai wa mutane miliyan 12, a kuma kawo karshen wasu ayyukan ceto, muddun masu bayar da gudunmowa ba su cika alkawuransu ba.
“Mun zaku mu samu kudaden da aka mana alkawari,” a cewar Lise Grande, shugabar shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Yemen, a wata takardar bayani a jiya Laraba. Ta kara da cewa, “Muddun kudi bai zo ba, mutuwa mutane za su yi.”
Wannan shekarar, daga cikin shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya 34 da ake yi a kasar ta Yemen, guda uku ne kadai aka samar da kudin gudanar da su.
Facebook Forum