Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magunguna 10 Da Citta Keyi A Jikin Dan'adam!


Ginger
Ginger

Duk dai da cewar anfi sanin itacen citta da yaji “Ginger” a turance, amma wannan yajin yanada matukara amfani a jikin mutun. Hakan yasa wasu masana sun gudanar da bincike akan irin magunguna da itacen citta keyi, musamman wajen bada lafiya mai nagarta ga mutane idan har anyi amfani da ita ta hanyar da suka kamata.

Gwararrun likitoci a yankin kasashen Asia, sun bayyanar da wasu magunguna guda goma, da itacen citta keyi. Sukace idan mutun nasamu matsalar narkewan abinci a cikin shi, ko ace mace nada juna biyu tana yawan amai, haka tana maganin jiri da kasalar jiki ga mace mai juna biyu. Kana idan mutun na fama da cutar Sankara, yana iya amfani da citta wajen jinyar cutar.

Itacen citta anyi ittifakin cewar yana da karfin da yake yakar wasu kananan cuttutuka da suke yawo a cikin jinin mutun, haka itacen citta kan kara dumin jikin mutun wanda hakan zai sa jinni ya dinga gudana yadda yakamata a kowane lokaci. Likitocin suka kara da cewar duk mutumin da ya rike amfani da citta to lallai zai samu lafiya mai nagarta.

Citta bata tsaya kawai a lafiyar ciki ba, har ma da yaki da cuttutuka da suke addabar mutane wajen kamuwa da mura da ma wasu cuttutka da sukan kama fatar mutun. A bincike da aka gudanar da yayi nuni da cewar citta na taimakawa wajen rage maikon da bashi da amfani a jikin mutun. Haka idan mutun na fama da ciwon gabobi, yayawaita amfani da citta wanda zata taimaka mishi so sai wajen samun lafiya, don haka akwai bukatar mutane su bada azama wajen amfani da itacen citta don gujema matsalolin maganin bature.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG