Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yayin Da Najeriya Ke Shirye-Shiryen Zaben Gwamnoni...


Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega

Wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta ce mutane akalla 500 suka mutu a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasa

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam da ke Nijeriya ta ce tashin hankalin da ya biyo bayan zabe ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 500, kuma hukumomi na shirin tarar yiwuwar karin tashin hankali a gobe Talata a zabubbukan matakin jihohi.

Kungiyar Civil Rights Congress ta Nijeriya ta fadi jiya Lahadi cewa akasarin tashin hankalin ya fi muni ne a arewacin Nijeriya musamman ma a jihar Kaduna.

Hukumomin Nijeriya dai na kin yin cikakken bayani game da tashin hankalin, gudan kar hakan ya iza karin tashin hankali. To saidai shaidu sun ce sun ga gawarwakin da aka kona a kan tituna da kuma wuraren ibada da su ma aka kona.

Tashin hankali ya barke bayan da Shugaba Goodluck Jonathan ya ci zabe a makon jiya, inda ya kada Muhammadu Buhari.

Mr. Buhari dai na kalubalantar sakamakon, to amman masu sa ido ‘yan ba-ruwa-na, sun ce an kamanta adalci a zaban.

Za a gudanar da zaben gwamnoni a Jihohin Nijeriya da dama a gobe Talata, im ban da a jihohin Bauchi da Kaduna. Hukumomi dai na ta kokarin tabbatar wa jama’a cewa fitowa kada kuri’a ba zata kasance da hadari ba.

XS
SM
MD
LG