Masu bincike da masana akan jiragen sama suna yiwa wani bangaren jirgin sama da aka gano a tsubirin Faransa dake kusa da Madagascar.\.
Ana kyautata zaton baragujin fukafukin jirgin saman da aka gani ka iya zama na jirgin saman kamfanin Malaysia Airlines da ya bace a watan Maris din shekarar 2014.
Idan ba'a manta ba jirgin ya taso ne daga kasar Malaysia akan hanyarsa ta zuwa kasar China sai ya bace. An yi watanni ana neman jirgin a karkashin tekunan yankin da ma wasu tekunan.
Jiya Laraba aka ga bangaren fukafukin wanda yake da tsawo kimanin mita biyu a wani tsibiri mai tazarar kilomita 3,500 daga tsibirin Madagasca. Masana sun tabbata baragujin na kiran samparin Boein777.
Kawo yanzu samparin Boeing 777 daya ne ya bace a duk fadin duniya. Wanda ya bacen kuwa shi ne na kamfanin Malaysia Airlines.
Kwararru daga kasar Faransa suna yiwa bagarujin binciken kwakwaf kafin su bada tabbaci ko na jirgin da ya bace ne mai lamba MH370.
To saidai wani kwararre daga Faransa Xavier Tytelman ya duba hoton baragujin kana ya shaidawa Muryar Amurka babbu shakka na jirgin sama samparin kirar Boeing 777 ne.