Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana zaton an tsinci ballin jirgin Malaysia da ya bata


Wasu iyalan fasinjojin bataccen jirgin Malaysia MH370
Wasu iyalan fasinjojin bataccen jirgin Malaysia MH370

An sami wani ballin jirgin saman da masu bincike suke kyautata zaton bangaren jirgin kasar Malaysia din nan ne mai lamba MH370, kirar samfurin Boeing 777 da ya bace a watan Maris, 2014.

Bangorin da aka yi amannar wani ballin fikafikinsa ne, an nufi kasar Faransa don yin bincike akai don gano gaskiyar kokwanton da ake. Kamfanin da yak era jirgin sun ce zasu shiga Faransa bisa neman izinin hukumomi don taya bin diddikin wannan lamari na jirgin da ya salwantar da mutanen cikinsa 239.

Mabincikan kasar Australia ma sun ce suna kyautata zaton bangorin jirgin ne na Malaysian Airline. Kamar yadda babban kwamishinan hukumar kula da lafiyar safarar kasar Australiyan Martin Dolan ya fadawa manema labarai a jiyan.

An dai tsinto ballin ne mai mita biyu a ranar Larabar data gabata daga bakin tekun tsibirin Reunion Island dake gabashin kasar Madagasca. Haka kuma kimanin tazarar kilomita 3,500 daga inda aka ji duriyar jirgin ta karshe a na’urar sadarwar da ke bin diddikin tafiyar jirage.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG