Yanzu haka an samu gawarwaki mutane goma sha takwas, a yayi rubata wanna labari
ba'a sami sauran mutne ba.
Wakilin,hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas Ibrahim Fariyola,yace sun sami kiran gaggawa ne da misalin karfe goma sha daya na dare ne,yace take suka shiga magana da sauran hukumomi dake iya bada gudunmawa game da wanna hadarin.
Sojojin ruwa,da masu kula da bakin iya kar teku da yan sanda masu sintiri cikin ruwa da kuma yan sanda masu kai daukin gaggawa suka hallara a wuridomin cigaba da aikin ceto.
An sami nasara tsamo wasu mutane da ransu,ko da yake wata mata daga cikinsu ta rasu akan hanyasu na zuwa asibiti.