Kungiyoyin suna zargi cewa an kwari Musulmai a jerin sunayen da gwamnati ta fitar. Cikin sunaye 492 kusan kashi 60 bisa 100 Kiristoci ne lamarin da suka ce idan an tsaya a hakan to za'a kwari Musulmai da addinin Musulunci.
A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi a Sokoto Majalisar Hadakar Kungiyoyin Addinin Musulunci ta Najeriya ko NACOMYO a takaice da ta Dalibai Musulmai ta Najeriya ko MSS a takaice sun bayyana rashin samun adalci ga Musulman Najeriya wurin tsayar da shawarwari a wurin taron saboda la'akari da yadda adadin wakilan taron mabiya addinin Kirista suka rinjayi na Muslmai da kusan kashi biyu bisa uku.
Shugaban kwamitin hadakar kungiyoyin Dr Sahabi Muhammed Jabo shi ya jagoranci taron da suka yi da 'yan jarida. Yace sun lura Kirista sun fi Musulmai rinjaye a jerin sunayen wakilan taron inda za'a cimma wasu batutuwa dake da mahimmanci. Yace idan an samu rabuwar ra'ayi za'a ce a yi kui'a to a nan idan abun da ya shafi addinin Musulunci ne ko rayuwar Musulmi za'a sha da su. Yayi kwatanci da jihar Kano dake da mutane fiye da miliyan tara da kuma jihar Bayelsa mai mutane miliyan daya da 'yan kai amma kowace jiha wakilai uku gareta.
Da alama kuma kungiyoyin sun yi mu'afaka da taron dattawan arewa da aka gudanar ranar Litinin da ta gabata a Kano. Taron ya tattauna ire-iren wadan nan korafe-korafen kamar yadda Barrister Dalung ya bayyana. Yace akwai rata tsakanin wakilan Kirista da Musulmai da aka nada. Kiristoci sun fi Musulmai yawa da kuasn mutane dari. Yace domin haka korafe-korafen na neman adalci ne domin sun ga za'a cucesu. Yace a nasu bangaren na dattawan arewa basu ma yadda da taron ba. Yace suna kallon taron kamar kungiyar yakin neman zabe ne. Yace idan taro ne na Allah da Annabi mutane arewa sun fi kowa yawan mutane. Misali arewa nada jama'a fiye da miliyan 75 amma an bata wakilcin kashi 33. Kudancin kasar dake da mutane miliyan 60 da 'yan kai tana da wakilcin kashi 65. To kenan ta bangaranci an zalunci arewa.
Kungiyoyin sun kira ga 'yan arewa musamman Musulmai da su kauracewa taron.