Duk da karin wa'adin da hukumar tayi lamarin ba zai shafi ranar zaben ba kamar yadda ta tsara a jadawalin da ta fitar. Za'a yi zaben ranar 17 ga watan Mayu yadda malam Ismail Idris Garba kwamishanan yada labarai na hukumar ya bayyana.
Batun sasantawa da samun masalaha na cikin dalilan da suka kawo ma wasu jam'iyyu jinkirin shirya sunayen 'yantakaransu. Neman samun daidaitawa ya dauke hankalin jam'iyyar APC lamarin da ya sa bata iya shirya sunayen 'yantakararta ba cikin lokaci. Injiniya Abdullahi Muhammed Gwarzo shugaban riko na APC yace tsarin jam'iyyar ya tanadi yin masalaha da daitawa kafin a yi zabe. Bayan hakan duk wanda aka dauka daidai ne. Sun tsaya ne su tabbatar kowa an kare martabarsa da mutuncinsa. Dalili ke nan suka tabbatar an yi adalci. Yace yanzu kowa zai koma karamar hukumarsa domin ya zauna da masu ruwa da tsaki kan zaben.
Ita ma jam'iyyar PDP ta bada gyaran da jam'iyyar ta yi a matsayin hujjarta na kasa mika sunayen 'yantakararta cikin lokaci. Alhaji Idris Nagwamma shugaban rikon jam'iyyar yace sun shirya yanzu zasu shiga zabe a kananan hukumomi 44 kuma da yadda Allah jam'iyyar zata lashe duk kananan hukumomin. Dangane da tsaiko da suka samu yace hakan ya faru ne domin sabbin shugabanni da aka kafa ranar Laraba da ta gabata.
Ga rahoto.