Shahararren jirgin daukar fasinja sumfurin jet din, ya tashi daga Addis Ababa, babban birnin kasar a yau Asabar da wani sabon nau’in batir, da aka sarrafa shi ta yadda zai hana jirgin kamawa da wuta.
Hukumar Sufurin Jirgin Sama ta Amurka ce ta amince da sabon nau’in batir din a makon jiya, wanda hakan ya share fage ga sauran irin wannan jirgin su cigaba da tashi da zaran an saka masu sabon batir din.
Ministan Sufurin Japan ya amince a hukumance jiya Jumma’a, cewa rukunin wannan samfurin jirgin ya cigaba da tashi da zaran an sassaka sabon batir din.
A halin da ake ciki kuma, da yake magana da ‘yan jarida yau Asabar a birnin Tokyo na Japan, babban injiniyan samfurin jirgin Boeing kuma jagoran kare samfurin 787, Michael Sinnett, ya ce har yanzu ba a san musabbabin matsalar nau’in batirin farko ba, to amman wata nu’urar da aka makala ma sabon nau’in batir din zai hana jirgin kamawa da wuta ko da an sami matsalar batir.