Jama’ai sun fadi yau Asabar cewa da Shugaban masakar ta New Wave Apparels, Bazlus Samad da kuma Ciyaman din kamfanin Mahmudur Rahman Tapash na hannu. Ba tabbatar ko har an tuhume su ba.
‘Yan sanda sun kuma kama injiniyoyi biyu da su ka amince da tsarin ginin.
A halin da ake ciki kuma yawan mace-macen ya haura zuwa 325 a daidai lokacin da masu ayyukan ceto kuma da ke gajiye, ke cigaba da aiki ba-ji ba-gani don zakulo masu rai.
An ceto mutane da dama yau Asabar, kuma har yanzu masu aikin na kokarin kaiwa ga wasu mutanen da aka tabbatar sun makale cikin baraguzan ginin. An ceto mutane sama da 2400 tun bayan da ginin ya ruguje, wadanda akalla rabinsu sun sami raunuka. Masu ayyukan ceton na kuma zakulo gawarwaki daga baraguzan ginin.
‘Yan sanda sun ce mai ginin da kuma shugabannin masakar sun yi biris da gargadin da aka ba su a hukumance cewa a mutane su kaurace wa ginin, bayan da kwararrun dubagari su ka gano wasu tsagu a ginin ranar Talata.